10 Mayu 2021 - 13:58
​Chadi: Sojoji Sun Ce Sun Samu Nasarar Murkushe ‘Yan Tawaye

Sojojin kasar Chadi sun sanar da cewa, sun samu nasarar murkushe ‘yan tawayen arewacin kasar, kasa da wata guda bayan kashe Idris Deby.

ABNA24 : Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da babban hafsan hafsoshin sojin kasar Chadi Abdulkarim Dawud ya yi a yammacin jiya a birnin Njamina, ya bayyana cewa; sun samu nasarar murkushe ‘yan tawayen arewacin kasar, kuma wannan nasara ce ga kasar Chadi.

A yammacin jiya ne sojojin na Chadi suka shigo cikin birnin Njamina acikin motocin yaki da suka hada da tankoki da kuma motoci masu sulked a manyan makamai, inda suke tarera wakoki na samun nasara a kan ‘yan tawaye.

Baya ga haka kuma, sojojin sun gabatar da wasu mayakan ‘yan tawaye da suka kama a gaban manema labarai a babban sansaninsu da ke cikin birnin Njamina.

A ranar 19 ga watan Afirilun da ya gabata ne dai aka sanar da mutuwar tsohon shugaban kasar ta Chadi Idriss Deby, wanda ya kwashe tsawon shekaru 30 yana mulkin kasar, bayan harbinsa da bindiga da ‘yan tawayen arewacin kasar suka yi a lokacin da ake gumurzu da su a kusa da iyakokin kasar ta Chadi da Libya.

342/